Janar Dambazau da babban sifeton 'yansanda Solomon Arase da kwantrolan hukumar shige da fice da na gidan yari da na 'yansandan fararen kaya da ma wasu sun kai ziyarar gani da ido zuwa jihar Borno.
Tawagar na Borno ne domin duba lamuran da suka jibanci harkokin tsaro. Sun fara da fadar gwamnatin jihar kafin su gana da Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar ibn Garbai El-Kanemi.
Tawagar ta ziyarci sansanin 'yan gudun hijira dake Dalori wanda yake da ya kasance mafi yawan jama'a.Yana da 'yan gudun hijira fiye da 15,000 da suka hada da mata da kuma kananan yara.
Ministan Janar Dambazau ya yiwa 'yan gudun hijiran jawabi. Ya yabawa sojojin yakin sama da suka samar ma sansanin wajen kiwon lafiya da kuma daidaikun jama'a da suka bada tasu gudummawa.Yace zasu yi iyakar kokarinsu su ga mutanen sun koma garuruwansu cikin dan lokaci. Duk garuruwan da aka kwato za'a sa masu jami'an tsaro domin kada 'yan ta'ada su sake farmasu.
Da tawagar ta wuce jihar Yobe sai gwamnan Borno ya rabawa 'yan sakai ko kato da gora motoci da yi masu alkawarin daukan dawainiyar kudin asibitocinsu.
Ga karin bayani.