Wannan na cikin bayanai da shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Sanata Mohammed Ali Ndume ya tattara a ziyarasa wacce ita ce ta uku da ya kai yankunan da sansanoni ‘yan gudun hijira inda cikin hawaye ya ce bai zata zai iske ‘yan gudun hijira na Daware a irin halin da suke ciki ba.
Sanata Mohammed Ali Ndume ya shaidawa wakilin sashin Hausa a hirar da ya yi da shi cewa baya ga matsalar sake gina rayuwarsu daga burabuzan da suka tarar bayan komawarsu garuruwansu, akwai kalubale na sake dinke rarrabuwar kawuna da zaman doya-da-manja sakanin mabiya addinai da masu bin addini daya.
Wannan ya sa Murya Amurka ta nemi ji daga kungiyoyin sa kai irinsu kungiyar wanzar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinin Kirista da Musulumci ta kasa da kasa da Imam Dokta Mohammed Ashafa yakewa jagoranci wanda daya daga cikin nashihohin da kungiyar ke koyarwa shine na yafewa juna kamar yadda ta yiwa iyaye da ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sako kwanan nan.
Shi ma abokin aikinsa Pastor Dokta James Morgan Wuye ya ce a daya bangaren kungiyar ta yi tsayin daka wajen fadakar da shugabannin addinai muhimmancin mutunta juna ta hanyar shirya tarurrukan karawa juna sani musamman a jihohin da rikicin Boko Haram ya shafa.
Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5