Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram: Jami’an Tsaro Sun Bukaci ‘Yan Najeriya Su Kara Sa Ido


Zanga zangar da 'ya gudun hijira su ka gudanar a jahar Borno a kwanakin baya
Zanga zangar da 'ya gudun hijira su ka gudanar a jahar Borno a kwanakin baya

Jami’an tsaron Najeriya sun yi kira ga al’umar kasar musamman wadanda su ke yankin arewa maso gabashin da su kara sa ido saboda ‘yan ta’adda.

Wannan kira na zuwa ne kwana guda bayann wani hari da aka kai garin Madagali na jahar Adamawa, wanda ya halaka mutane da dama.

Har ila yau harin ya raunata dumbin jama’a da yanzu haka ke karbar magani a asibitoci daban-daban.

“Idan sun taho wadannan ‘yan kunar bakin wake ana iya gane su.” In ji darektan yada labaran dakarun sojin Najeriya, Janar Rabe Abubakar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajintawa iyalai da wadanda harin ya rutsa da su.

Bama-bamai biyu ne suka tashi a kasuwar ta Madagali, wadanda ake zargin wasu mata ‘yan kunar bakin wake guda biyu ne suka tayar da su.

Domin jin cikakken bayani, saurari rahoton wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka, Umar Faruk Ibrahim:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG