Su dai wadannan yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya raba su da garuruwansu a jihohin Borno da Adamawa, yanzu haka suna zaune ne a wata cibiyar jinya ta Gulun-clinic dake hanyar Kona, a wajen Jalingo fadar jihar Taraba, kuma suna zaune ne a cikin wani mawuyacin hali, inda suke neman a taimaka musu.
Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, ya ziyarci wannan sansani inda ya zanta da ‘yan gudun hijirar wadanda suka bayyana masa halin rayuwa da suke ciki. A cewar wata uwa mai suna Rufkatunal, yanzu haka suna shan matukar wahala wajen samun hanyar da zasu ciyar da kansu, domin yaransu kanana suke fita suna leburanci kafin su sami kudin sayen abinci wanda kuma baya isarsu. Shima wani magidanci a sansanin cewa yayi tabbas suna neman ababen rayuwa musamman abinci.
Shugaban ‘yan gudun hijirar na wannan sansani ya zargi gwamnati da nuna musu shakulatin bangaro da cewa tun lokacin da suka gudo Taraba ba a waiwayesu ba. duk da cewa kungiyoyin daban daban sunje sun dubasu, itama gwamnatin tarayya ta tura jami’anta amma har yanzu shiru.
Kawo yanzu dai kungiyoyi da kuma ‘yan rajin kare hakkin dan Adam sun fara mayar da martani. Rev Sabelo Andrew, dan fafutuka ne a jihar Taraba, ya bukaci hukumomin kai dauki da suke tunawa da wadannan al’ummu.
Ana ta bangaren hukumar kai dauki ta jihar, tace su suna nasu kokari to amma rashin kudi na cikin matsalolin dake taka musu birki ta jihar kamar yadda babban sakataren hukumar Mr Nuvalga Danagbo ya bayyana.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5