Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Taki Amincewa Buhari Ya Ciwo Bashi


Dr. Bukola Saraki shugaban majalisar dattawan Najeriya
Dr. Bukola Saraki shugaban majalisar dattawan Najeriya

Makon jiya ne shugaban Najeriya ya gabatarwa majalisar dattawa bukatar ciwo bashin dalar Amurka biliyan talatin ya cike gibin dake cikin kasafin kudin bana domin ya samu ya aiwatar da ayyuka da zasu taimaka wurin farfado da tattalin arzikin kasa.

Shugaban masu rinjaye a majalisar Ali Ndume yace kin amincewa da bukatar shugaban kasa da majalisar tayi ya bashi mamaki.

To amma Sanata Ali Ndume tamkar yayi amai ya lashe ne yayinda ya dorawa ofishin shugaban kasa laifi akan dalilin da ya sa majalisar bata biya masa bukata ba. Yace wasikar da shugaban ya aiko masu bata kunshi cikakkun bayanai ba. Yace babu bayanan da suka kamata a hada a ba kwamitin da zai yi nazari akan bukatar.

Wasikar shugaban kasa bata bayyana inda za'a ciwo bashin ba, kazalika shekaru nawa za'a yi ana biyan bashin da kuma kason da za'a biya kudin ruwa. Baicin wadannan yakamata a san sharudodin dake tattare da bashin. Ali Ndume yace bata yiwuwa majalisa ta amince da bukatar ido a fufe.

Ali Ndume yace bashin ba na cikin gida ba ne. Daga waje za'a karboshi kuma yana iya kawo matsala irin wadda ya sa kasar ta sha da kyar yayinda ta ciwo bashi daga kasashen waje.

Sanata Ita Enang mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin majalisa yace sun ji korafin sanatocin kuma zasu yi iyakar kokarinsu su bada duk takardun da suke bukata.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG