Bayanai na nuni da cewa lamarin ya auku ne da yammacin jiya Talata a wani wuri da ake kira da Turanci “Many Have Gone” wato da yawa sun tafi.
Wani da ya shaidi lamarin kuma ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ya ga gawarwakin ‘yan sanda shida, wasu da dama kuma sun sami raunuka, yayin da wasu suka gudu zuwa daji don tserar da ransu.
Ya ce a lokacin da motocin ayarin mataimakin gwamnan suka iso sun samu motoci tsaye a kan hanya, wasu motocin jami’an tsaro dake tare da gwamnan sun yi kokarin bude hanya, nan ne maharan suka bude wuta a kan motocin suka kashe ‘yan sanda, lamarin da ya kuma yi sanadin juyawa da mataimakin gwamnan zuwa Lafia.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Nasarawa, Ismail Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce an sami rasa rai, sai dai ba su tantance yawan wadanda suka rasu ba.
Kakakin ‘yan sandan ya ce ba ana auna mataimakin gwamnan ba ne; illa hari ne na masu fashi. Ya kuma ce kwamishinan ‘yan sanda ya je wurin kuma ya bada umarni ga kwamandodin rundunar ‘yan sandan yankin Akwanga da su kara daukar matakan hana sake faruwar haka a wurin.
Ga Zainab Babaji daga Jos da karin bayani:
Your browser doesn’t support HTML5