'Yan Fashi da Makami Sun Kai Hari Kan Wata Kasuwa a Mubi

At least 60 people were also injured in the attack.

Wasu 'yan bindiga da ake zato 'yan fashi da makami ne sun yiwa wata kasuwa a Mubi kawanya lamarin da ya rutsa da mutane da dama da asarar kadarori na dubban miliyoyin nera.
Kamar yadda wasu 'yan kasuwar suka tabbatar mutane a kalla goma ne suka rasa rayukansu a wannan harin da 'yan bindigar suka kai. Wasu kuma da yawa suka jikata.

Mutanen da suka kai harin wani ganao da ya sha da kyar ya ce mutanen dogaye ne kuma suna cikin fararen kaya kodayake akwai wasu sanye da bakaken kaya.

'Yan bindigar sun yiwa kasuwar kawanya ne domin shiga kasuwar daga duk kofofinta. Da suka shiga kasuwar sai suka jefa wani abu kamar guruneti cikin shagon da ake sayar da tufafin mata wanda nan da nan ya kama wuta kafin su soma harbe-harbe na mai kan uwa da wabi. Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kashe mutane biyar yayin da suma suka rasa mutane biyar cikin wani musayar wuta da jami'an tsaro.

Maharan sun kwace dukiyoyi daga hannun mutane da karfin bindiga. Alhaji Muhammed Nuru shugaban 'yan canji na kasuwar ya ce kawo yanzu dai an kashe mutane da dama domin sun shigo ne daga kowace kofa. Ya ce bayan sun kone kursiyoyin kasuwar sai suka kama harbi kana su 'yan kasuwan suka kama gudu. Ya ce sun bi 'yan canji da bindiga suna fasa akwatunansu suna kwashe kudi. Wadanda kudinsu na cikin sef sai suka sa masu bindiga a ka dole suka bude barayin suka kwashe kudadensu. Ya ce ta wurin gefensa abun da barayin suka sace ba zai kasa nera miliyan ashirin ba. Yanzu suna zaman dar dar ne domin 'yan kasuwa duk sun rufe shaguna sun koma gidajensu.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Fashi da Makami Sun Kai Hari Kan Kasuwar Mubi - 2:14