'Yan Fashi Da Makami Sun Fara Kai Hari Da Tsakar Rana

'Yan Fashi

Yanzu haka ‘yan fashi da makami sun fara afkawa jama’a da rana kiri-kiri, ta hanyar amfani da bindigogi musamman a kewayen bankuna. Dalilin da yasa kwamitin tsaron yankin na Yamai kiran taron gaggawa a karkashin jagorancin Gwamnan Yamai Issaka Hassan domin neman mafita.

Daya daga cikin wannan al'amuran shine wanda ya faru a jiya Alhamis, a kofar wani bankin dake tsakiyar birnin Yamai, inda wasu mutane biyu akan babur suka bude wuta kan wani mutun bayan ya ciro kudaden da aka kiyasta cewa sun kai miliyan 49 na cfa.

A take wannan bawan Allah ya fadi kasa jina jina, daga nan su kuma barayin suka arce da jakar kudin dake hannun sa. Wannan dalilin ne yanzu ya jefa jama’a cikin zullumi.

Al'amarin ya farune kwana 1 bayan da wasu ‘yan bindiga 2 akan babur suka harbi wani mutun shi ma, a kofar wani asibiti kudi dake anguwar Yantala. Shi kuma sun biyo shine daga bankin da ya ciro 500.000 na cfa. Wannan matsalar da wani matashi Abdourazak Hamidou ke gani da zaman kashe wandon matasa a ciki.

'Yan sanda har sun kaddamar da bincike domin gano ainihin mabuyar wadannan ‘yan fashin. A lokacin da bangare kwamitin tsaron yankin Yamai ke gudanar da taro a wannan Juma’ar, karkashin shugabancin gwamna Issaka Hassan Karanta, wanda bai bada karin bayani ba har sai nan gaba.

Souley Moumouni Barma ya hada muna wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Fashi Da Bindiga Sun Fara Hari Da Tsakar Rana A Birnin Yamai