A zamanta ta wacce take kan gaba a kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a tsakanin magoya bayan jam'iyyar Democrat, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a zahiri da badini ita ce a tsakiya, domin a yadda aka jera su, ita ce a tsakiyar sauran 'yan takarar hudu.
A kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a na bayan bayan nan sakamko ya nuna Hillary ce take kan gaba da maki 40 cikin dari, sannan babban wanda yake kalubali takararta Sanata Bernie Sanders shine yake biye d a ita da maki 25.
Ita dai Madam Clinton wacce take kan gaba aka jefawa tambaya mafi wuya, cewa tana yawan canza ra'ayinta domin a zabeta. An bada misali da yarjejeniyar cinikayya ta baya bayan nan da ake kira TPP, da kasashe 12 dake yankin Pacific suka sanya hanu akai.
Madam Clinton ta yarda cewa lokacinda take sakatariyar harkokin wajen Amurka ta goyi bayan shirin, ta kara da cewa yanzu bayan shekaru ana shawarwari kan yarjejeniyar, daidaiton bata cika mizani na auna shirin ba.
Da aka tambayesu su duka 'yan takarar biyar abu mafi muhimmanci da ya fuskanci Amurka, 'yan takarar kowa ya bada amsa daban da na dan uwansa.Dan takara Lincoln Chafee wanda tsohon gwamnan jihar Rhode Island ne ya amabci rikicin da ake yi a gabas ta tsakiya. Martin Omalley, tsohon gwamnan jihar Maryland ya zabi matsalar rikicin Nukiyar Iran, Sakatariya Clinton ta zabi barazanar Nukiliya a duniya baki daya, Senata Bernie Sanders ya dauki batun canjin yanayi.Shi kuma tsohon Senata Jim Webb ya nuna danganatakar Amurka daChina da kuma barazanar tsaro a internet da kasar Sin din take yiwa Amurka.
Ba kamar takwarorinsu na Jamiyyar Republican ba, su 'yan takarar na jam'iyyar Democrat basu bata lokaci suna sukar juna ba, sunyi amfani da zarafin na jiya Talata wajen bayyana manufofinsu da irin ayyuka da suka yi a baya.