Kungiyar hana kamfanonin musayar kudaden kasashen waje da aka fi sani da Bureau De Change, reshen jihar Kano ta kuka kan matakan da Babban Bankin Najeriya ke dauka na shawo kan matsalar faduwar darajar Naira.
Kungiyar tace akwai kura kurai a matakan da Babban bankin ke dauka, bisa ga cewar kungiyar, wannan matakin ba alheri bane ga kasar, a maimakon haka, zai gurguntar da tattalin arzikin kasa. Mataki na baya bayan nan dai da babban bankin Najeriya ya dauka shine na hana kamfanonin musayar kudaden kasashen waje bude ressa a wadansu wurare na kasar, da mallakar shaidar ilimin digiri, domin aiki a kamfanonin musayar kudaden na waje.
Wannan matakin dai a cewa, kungiyar zai raba dubban membobinta da ayyukansu, a wannan lokacin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke kokarin samarwa miliyoyin matasa da ayyukan yi, ko kuwa basu kudin zaman kashe wando na naira dubu biyar a wata.
A hirarsu da Muryar Amurka, daya daga cikin ‘ya’yan kungiyar ya bayyana cewa, akwai lauje cikin nadi, game da matakan da ake dauka na yiwa harkar ‘yan canji gyara. Yace abinda suke gani shine, ana neman sannu a hankali a kauda ‘yan arewacin Najeriya dake wannan harkar a maida ita hannun gwamnati da kuma wadansu manyan mutane.
Ya bayyana cewa, daukar wannan matakin bashi da wata nasaba da yunkurin gwamnatin na shawo kan matsalar cin hanci da rashawa da kuma dakile warurar kudaden gwamnati. Bisa ga cewarsa, kawo yanzu ba a sami ko mutum daya dake wannan sana’ar da hannu a badakalar kudin da ake tuhumar wadansu jami’an gwamnatin da ta shude ba. Yace wadanda ke warurar kudaden ba zuwa suke su nemi canji a irin wadannan kamfanoni ba, suna samunshi ne kai tsaye daga bankuna.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Babangida Jibrin ya aiko daga Lagos.
Your browser doesn’t support HTML5