'Yan mazhabin Shi'a na jamhuriyar Nijar sun hallara a masallacin Shahid Karbala dake birnin Yamai, domin yin addu'a tare da jajantawa 'yan'uwansu dake Najeriya, a bayan wani farmakin da sojoji suka kai ma cibiyar 'yan mazhabin a garin Zaria a Jihar Kaduna.
A lokacin da yake huduba ga dubban maza da mata da suka halarci wannan taron nuna alhinin, madugun 'yan mazhabin Shi'a na Nijar, Sheikh Ahmed Lazare, yace da'awarsu ta hankali ce ba ta tayar da fitina ba, don haka ba su yin amfani da makami.
Yace shi ma kansa shugaban 'yan Shi'ar na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya sha nanata cewa akida ba a kawar da ita da makami ko da harsashi, sai ta wa'azi.
Wata 'yar Najeriya dake karatu a wata jami'a a Yamai, Wasila Salisu Funtua, ta bayyana mamakin irin kashe-kashen na Zaria, tana mai cewa sun fi shekaru aru aru su na gudanar da irin wannan taron amma ko sau daya ba a taba ganinsu da wani makami ba.
Shi ma Sheikh Lazare ya nanata cewa akidarsu ta zaman lafiya ce, yana mai fadin cewa daga cikin dukkan kungiyoyi masu aikata ta'addanci a duniya, babu ta 'yan Shi'a.
Al'ummar Nijar dai su na nuna damuwa sosai kan wadannan abubuwan da suke faruwa a mnakwabciyarsu Najeriya, musamman batun Boko Haram da kuma wannan sabon rikicin dake kara yin muni na 'yan mazhabin Shi'a.
Wakilin Sashen Hausa, Souley Moumouni Barma, ya aiko da cikakken rahoto.