Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Afirka ta Tsakiya: An Yi Zaben Raba Gaddama Kan Sabon Kundun Tsarin Mulki


Layin zabe a Afirka ta Tsakiya
Layin zabe a Afirka ta Tsakiya

Duk da samun kisan kai da aka yi a Afirka ta Tsakiya an gudanar da zaben raba gardama akan sabon kundun tsarin mulkin kasar.

Akalla mutane shidda ne suka mutu a jiya Lahadi yayin wata arangama da aka yi a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, a lokacin da ake zaben raba-gardama kan sabon kudin tsarin mulkin kasar da ake sa ran zai kawo karshen tashin hankalin da kasar ta kwashe fiye da shekaru uku ta na fuskanta.

Wani dan jaridan kamfanin dillancin labaran kasar Faransa, ya ce ya ga gawarwaki biyu da kuma wasu da dama a masallaci, sai dai babu wani rahoto a hukumance da ya nuna cewa an samu wadanda suka jikkata dalilin zaben da aka yi.

Dama dai, mayakan sa kai a bangarorin Musulmai da Kirista, wadanda ake zargi da haddasa rikicin, sun sha alwashin hana wannan zabe.

Sai dai wakilin Majalisar Dinkin Duniya da ke Bangiu, babban birnin kasar, wato Parfait Onanga- Anyanga, ya yaba da irin na-mijin kokarin da mutanen kasar suka yi, wajen fita su kada kuri’unsu duk da irin barazanar da aka yi na warzaga zaben.

Idan dai har aka amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar, hakan zai kayyade wa’adi biyu na shekaru biyar-biyar ga shugaban kasa, kuma ya ba da walwalar yin addini.

XS
SM
MD
LG