Rahotannin dai na cewa tun a ranar Asabar ne mayakan Boko Haram suka soma kai farmaki a wasu kauyuka na karamar hukumar Madagali, inda suka yi barna tare da kwashe shanu kusan 700.
Haka kuma, rahotanni sun tabbatar da cewa wasu tagwayen bama-bamai sun sake tashi a jiya lahadi a kauyen Silda.
Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaye sunan shi, ya ce yanzu haka suna cikin halin dar-dar, sakamakon abubuwan dake faruwa cikin kwanakin nan.
Koda yake hukumomin tsaro basu yi Karin haske ba ya zuwa lokacin hada hancin wannan rahoto, to amma dan majalisar wakilai dake wakiltar Madagali, da Michika, Mr Adamu Kamale, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bukaci akai musu dauki.
Shima dai shugaban karamar hukumar Madagalin Yusuf Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ko a safiyar yau ma sai da ‘yan sakai na maharba suka tarwatsa wani harin.
Domin karin bayani, sau rari rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.
Your browser doesn’t support HTML5