Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin PDP Yaki Ci Yaki Cinyewa


PDP
PDP

Yanzu haka dai da alamun babu sauki a rigimar cikin gida dake akwai a babbar jam’iyar adawa ta PDP reshen jihar Adamawa,

Yayin da ake haramar gudanar da zaben shugabanin jam’iyar a jihar Adamawa, wato State Congress da aka shirya gudanarwa a gobe asabar, wasu kusoshin jam’iyar sun ce ba zata sabu ba,wai bindiga a ruwa.
'Yayan jam’iyar sun yi zargin cewa ana kokarin yin sabi dora ne a zaben na gobe.
A wajen wani taron manema labarai,kusoshin jam’iyar sun zargi yan kwamitin riko a jihar da nuna wariya,da kuma yunkurin sabi –dora, wanda suka ce ba zasu amince ba.
Dr Umar Ardo daya daga cikin kusoshin jam’iyar ya ce su ba zasu amince ba,kuma tuni suka garzaya kotu.
Shima wani madugun ‘yan talauyen PDP a jihar Chief Medan Teneke, yace duk da wannan matsalar da suke fuskanta a yanzu su suna nan daram a jam’iyar PDP.

Hon Lumsambani Dilli shi kadai ne dan jam’iyar PDP a majalisar dokokin jihar ya ce abun takaici ne abubuwan dake faruwa a jam’iyar, musamman a jihar Adamawa.

Ya zuwa yanzu yan kwamitin riko na jam’iyar a jihar sun ce ba zasu ce komi ba a yanzu ba, to sai dai kuma a martaninsu ‘yan daya bangaren,wato bangaren su Baba Joel sun musanta korafen da ake yi, kamar yadda Hon Abdullahi Prembe ya bayyana.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG