Cikin 'yan kwanakin nan jami'an sojin Najeriya na ta barin wuta ga 'yan bindigan yankunan jihar Zamfara, abin da wasu ke alakantawa da dalilin kwararar 'yan-bindigar daga yankin zuwa makwabta.
Dan-masanin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Idris Abdurra'uf, ya ce sun fara samun rahotannin ganin wucewar 'yan bindigar a wasu yankunan Birnin Gwari tun daga ranar Laraba.
Abdurra'uf ya ce 'yan bindigar da ake tunanin sojoji ne su ka fatattako su daga Zamfara, suna ta shiga yankunan Birnin Gwarin akan babura dauke da makamai.
Tun ba yau ba, masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya, na ganin dole sai jami'an tsaro sun sauya salo kuma har yanzu ya na kan wannan matsayi.
Manjo Shinko ya ce dole ne gwamnati ta kara jami'an tsaro a yankin Birnin Gwari, kuma duk lokacin da sojoji za su kai wa 'yan bindiga hari to a girke jami'an tsaro a iyakokin da su ke wucewa don karasa su.
Dama dai gwamnan jihar Kaduna Malam Nasuru Ahmed El-rufa'i, ya sha nanata bukatar ganin an dauki matakin bai daya a dukkanin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan bindigar da ya ce hakan ne kawai mafita.
Yankunan karamar hukumar Birnin Gwari da dama dai na fama da hare-haren 'yan bindigar, da a bana ma su ke barazanar hana su noma baya da maida hanyar Kaduna zuwa Birnin tarkon mutuwa da kusan duk mako sai sun tare matafiya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5