‘Yan bindigan dai sun yi garkuwa da dan' uwan na Jonathan mai suna Jephthah Robert ne a cikin gidansa da ke birnin Yenagoa, fadar gwamnatin jihar Bayelsa.
Rahotanni daga jihar Bayelsa sun yi nuni da cewa, ya zuwa yanzu ,babu wani labari daga wadanda suka yi awon gaba da dan uwan na Jonathan.
Tun ranar litinin ne 'yan bindigar suka yi garkuwa da Jephthah kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A bangaren matakin da jami’an tsaro su ka fara dauka don kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi din, rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta bakin kakakinta, SP Asinim Butswat, ta tabbatar da batun yin garkuwa da dan uwan na tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan.
Rundunar dai ta ce tana yin duk mai yiyuwa wajen tabbatar da cewa an ceto Jephthah tare da kama miyagun irin da ke da hannu a sade shi.
Haka kuma, a yanayin da ake ciki dai babu cikakken bayani a game da yadda ‘yan bindigar suka kutsa cikin gidan Jephthah kuma suka yi awun gaba shi.
Rahotanni dai sun yi nuni da cewa, matsalar yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa musamman a baya-bayan nan ya karu a mahaifar tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan wato jihar Bayelsa.
Ana kyautata zaton cewa, akwai yiyuwar wasu gungun masu tace mai ta haramtattun hanyoyi a kauyen Jonathan na da hannu a cikin wannan danyen aiki sakamakon yunkurin da Jephthah ya yi na dakatar da haramtattun ayyukansu.
Tun shekarun baya dai, yankin Neja Delta na fama da matsalolin da suka shafi garkuwa da mutane domin neman kudin fansa kafin matsalar ta zama annoba a yankin arewa maso yamma da tsakiyar Najeriya wanda ya rikide zuwa kashe-kashen yan bindiga a yankin arewa maso yamma din.
Gwamnatin Najeriya dai na yin duk mai yiyuwa wajen ganin karshen matsalar a kasar kamar yadda ta sha fada ta bakin masu magana da yawunta.