‘Yan Bindiga Sun Sako Karin Yaran Makarantar Bethel Baptist 10

'Yan Bindiga

Yan bindigar da suka sace yaran makarantar Bethel Baptist da ke Damishi a jihar Kaduna sun sake sakin karin wasu dalibai 10 daga cikin 21 da ke tsare a hannunsu, bayan shafe kwanaki 81 da aka yi garkuwa da su.

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya wato CAN reshen jihar Kaduna, Rabaran Joseph Hayab, ya cewa an saki karin daliban 10 ne a ranar Lahadi kumar har an sada su da iyayensu kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

Wannan labarin na zuwa ne a daidai lokacin da dan majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, a karshen mako, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan kisan da wasu ‘yan Boko Haram suka yi wa wasu sojojin Najeriya a kwanakin baya-bayan nan a karamar hukumar Marte-Dikwa ta jihar Borno.

A yayin da yake ba da karin bayani game da daliban Bethel da aka sako, Hayab ya yi fatan cewa nan ba da dadewa ba yan bindigar za su saki sauran dalibai 11.

Hayab ya yi godiya ga dukkan 'yan Najeriya akan addu'o'insu da goyon baya da suka nuna tun bayan sace yaran, yana mai cewa sun dogara ga Allah cewa sauran za su fito nan ba da jimawa ba.

Idan ana iya tunawa, a ranar 5 ga watan Yuli ne 'yan bindigar suka mamaye makarantar da ke da nisan kilomita shida daga garin Kaduna inda suka sace dalibai 121.

Tuni dai 'yan ta'addar suka yi ta sako daliban rukuni-rukuni har hudu, inda a halin yanzu sun sako dalibai 110 hade da wadanda suka sami kafar tserewa daga hannunsu.

Rahotanni daga jihar Kaduna dai sun yi nuni da cewa iyayen daliban sun biya sama da naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa ga 'yan bindigar kafin a sako ‘ya’yansu, kuma a bisa duk rukunin daliban da aka sako iyaye ke biyan sabon kudin fansa.

Hedikwatar rundunar 'yan sandan Najeriya da ke birnin Abuja ta gabatar da mutane uku da ake zargi da hannu a sace daliban na makarantar Bethel Baptist.