Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutum Guda, An Sace Wasu Uku a Wata Majami'ar Kogi


DIG Usman Alkali Baba.
DIG Usman Alkali Baba.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari wata majami'ar ECWA a Kogi, inda su ka yi awon gaba da wasu mutane uku, su ka kuma kashe wani mutum.

A ci gaba da kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta, wasu 'yan bindiga sun kai hari wata Majami'ar ECWA a jihar Kogi, inda su ka bindige wani har lahira, su ka kuma sace wasu mutane uku.

Wannan Hari dai da aka Kai da sanyin safiyar Lahadin a Majami'ar ECWA da ke garin Kabba, ya yi matukar tayar da hankalin mazauna yankin. Malam Dan Asabe Lokaja, mai Lura da Al,amuran yankin ya ce Maharan sun kashe Mutun guda tare sace wasu Kimanin 5; Kamar yadda ya yi karin bayani a sautin da wakilin Muryar Amurka ya nada.

To kokarin jin ta bakin Rundunar 'Yansandan jihar kogin ya ci tura domin kuwa Kakakin Rundunar 'Yansandan jihar kogin, Mr.Williams Aya bai dauki waya ba,

To amma Gwamnatin Jihar kogin ta tabbatar da aukuwar lamarin. Sai dai Kwamishinan Labarai na jihar, Kindly Panwo ya ce Maharan ba sun kai hari a Majami'ar ba ne musamman. Sun samami wani ne a cocin.

Da ya ke magana akan Nasarar da aka samu a yaki da 'yan bindiga a jihar Kogin kuwa Kwamishinan Labaran, Mr.Panwo ya ce gamayyar Jami'an tsaro da suka hada da 'yan banga, sun samu nasarar hallaka 'yanbindigar da dama tare da samun nasarar kubutar da mutane uku da 'yanbindigar su ka yi garkuwa da su; kamar yadda ya yi karin bayani a saudin da wakilin Mureyar Amurka ya nada.

Ya ce abin takaici daga cikin wadanda Jami'an tsaron suka kama har da wani mai kai wa 'yanbindigar makamai wanda ma jami'in tsaron farin kaya ne na Sibil Difens. Ga Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG