Satar shanu ta zama ruwan dare a Najeriya da haka ke ciwa mutanen kasar tuwo a kwarya musamman ma fulani makiyaya.
WASHINGTON DC —
Baya ga matsalar tsananin rashin tsaro a Arewa maso Gabas da ke da alaka da ta’addanci. satar shanu na daya daga cikin abinda ke ciwa mutanen Borno tuwo a kwarya.
Alhaji Ibrahim Ahmed tsohon magatakardar kungiyar Miyetti Allah ya fadawa wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Haruna Dauda Biu cewa an sace musu shau dubu daya da dari biyar, sai tumaki dari shida da talatin da biyar.
Wasu fulanin da abin ya ritsa da shanunsu, sun bayyana yadda abin ya faru bayan da mutanen da ke dauke da bindigogi suka farraka su suka kora ababen kiwon nasu. Ga cikakken rahoton daga kasan wannan shafin.
Your browser doesn’t support HTML5