'Yan Bindiga Sun Sace Sarkin Kajuru Da Wasu Mutane 13 A Kaduna

Gunmen

Rahotannin daga jihar Kaduna sun yi nuni da cewa, wasu ‘yan bindiga sun afkawa masarautar Kajuru dake yankin kudancin jihar inda suka yi awon gaba da Sarkin garin, Alhaji Alhassan Adamu, dan cikinsa 1, jikokinsa 4 da wasu mutane 7 a gidaje makwabta da ke fadar.

‘Yan bindigan sun afkawa masarautar da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna ne da misalin karfe 12 da mintin 25 na sanyin safiyar yau Lahadi kamar yadda wani dan uwan sarkin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa wakilinmu a jihar, Isa Lawal Ikara.

Dan uwan sarkin na Kajuru, ya ce 'yan bindigan masu tarin yawa da ba su iya tantance adadinsu ba sun far wa masarautar bayan mamaye garin da sanyin safiyar yau Lahadi, lamarin da ya sa mutanen garin ba su iya daukar wani mataki ba sakamakon fargabar fadawa a hannun maharan.

Majiyoyi dai sun yi nuni da cewa, a cikin minti 30-40 ne 'yan bindigan suka balle kofar shiga fadar suka kutsa cikin dakin sarkin tare da yin awon gaba da shi da sauran wasu mutane 13 hade da suka hada dansa daya, da jikoki hudu.

Wannan lamarin dai na zuwa ne kwanaki shida bayan sace yaran makarantar Bethel Baptist dake makwabta da karamar hukumar Chikun dake da nisan kilomita 30 da fadar gwamnatin jihar ta Kaduna.

A yayin tabbatar da afkuwar lamarin ga jaridar Channels, kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce tawagar hadin gwiwar sashe rundunarsa da dama sun kaddamar da aikin ceto sarkin mai shekaru 85 a duniya da sauran mutane da ‘yan bindigan suka sace.