‘Yan Bindiga Sun Sace Iyalan Wasu 'Yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina

Gunmen

Bayan 'yan sa’ao’i da sace wani dan majalisar dokokin jihar Katsina, wasu ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Tafoki na karamar hukumar mulkin Faskari, inda suka yi awon gaba da kanwar mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar, Shehu Dalhatu Tafoki.

Dan majalisar Shehu Tafoki ya tabbatarwa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin, inda ya ce da sanyin safiyar ranar Lahadi bata-garin suka kai farmakin.

Tafoki ya ce kanwarsa da aka sace ’yar makarantar sakandare ce kuma ana kan shirin daura aurenta.

Rahotanni daga kauyen Tafoki sun bayyana cewa yan bindigar sun kai hari a kauyen ne da misalin karfe 1 na dare inda suka shiga gidan mai gari wanda shi ne gidan iyayen dan majalisar kai tsaye sannan suka sace kannensa mata biyu.

Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa a yayin da 'yan bindigar ke kan hanyarsu ta arcewa zuwa cikin daji sun yi taho-mu-gama da ’yan banga inda suka yi ruwan wuta a tsakaninsu lamarin da ya kai ga daya daga cikin matan da aka sace ta tsere ta dawo gida, inda suka tafi da dayar kamar yadda Tafoki ya bayyana.

A wani bangare kuma, wasu mutane da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki gidan dan majalisar dokokin jihar ta Katsina mai wakiltar karamar hukumar Bakori, Dakta Ibrahim Kurami da yammacin ranar Asabar, inda suka yi awon gaba da matarsa da ‘ya’yansu biyu.

Rahotanni sun yi nuni da cewa 'yan bindigar sun far wa gidan dan majalisar da ke kauyen Kurami na karamar hukumar Bakori ne da misaling karfe 9 da minti 15 na dare, inda suka harbi wani mutum da suka samu a bakin babbar kofar gidan inda suka bar shi da raunin harbin bindiga.

Har ya zuwa lokacin hada wannan labarin, Tafoki ya ce ’yan bindigar ba su neme su ba.

Hakar mu ba ta cimma ruwa ba a kokarin ji ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa, kan lamarin.