Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan bindiga Sun Kashe Kanin Sowore, Sun Yi Garkuwa Da Mutum Biyar


Marigayi Olajide Sowore (Facebook/Omoyele Sowore)
Marigayi Olajide Sowore (Facebook/Omoyele Sowore)

Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewa maso yammacin kasar, inda ‘yan bindiga suka mayar da satar mutane don neman kudin fansa tamkar sana'a.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe Olajide Sowore, kani ga mai fafutukar kare hakkin bil adama kuma mawallafin jaridar yanar gizo ta Sahara Reporters Omoyele Sowore.

A ranar Asabar ‘yan bindigar suka harbe Olajide har lahira a kusa da yankin Okada da ke jihar Edo.

“Yana kan hanyarsa ta komawa Benin inda yake karantar ilimin hada magunguna a Jami’ar Igbinedion a lokacin da abin ya faru” In ji Omoyele Sowore.

Sowore har ila yau ya rubuta cewa “rahotanni sun ce makiyaya ko masu garkuwa da mutane,” ne suka kashe kanin nasa.

Omoyele Sowore (Facebook/Omoyele Sowore)
Omoyele Sowore (Facebook/Omoyele Sowore)

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin ‘yan sandan jihar ta Edo Bello Kotongs ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Kotongs ya ce harin ya faru ne a yankin Isawa akan hanyar Legas zuwa Benin da misalin karfe 6:45 na safiyar ranar Asabar.

Kakakin ya kuma kara da cewa, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutum biyar da ke tafiya tare da marigayin.

Wannan lamari na faruwa ne kwana guda bayan da wasu ‘yan bindiga suka shiga makarantar sakandare ta Kaya da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, suka sace dalibai sama da 70.

Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a Najeriya musamman a arewa maso yammacin kasar, inda ‘yan bindiga suka mayar da satar mutane tamkar sana'a.

Lamarin ya kai ga har suna sace dalibai da malamansu, abin da ya sa gwamnatocin jihohin yankin arewa maso yammaci da dama suka rufe makarantu har da ma kasuwanni.

XS
SM
MD
LG