'Yan Bindiga Sun Mamaye Kauyukan Wase Da Kanam A Jahar Filato

Wasu yan bindiga

Al’ummomin wasu yankunan dake kananan hukumomin Wase da Kanam a Jahar Filato sun koka kan yadda ‘yan bindiga ke kisan mutane suna sace dabbobi da yin garkuwa da mutane a kauyukansu.

A cikin ‘yan kwanakin nan, lamarin tsaro ya tsananta a kauyukan dake kan iyakokin jihohin Filato, Taraba da Bauchi, inda ‘yan bindiga suka tsaurara kai hare-hare suke kuma sace mutane, dabbobi da kisan mutane.

Shugaban kasuwar shanu na garin Jarmai a karamar hukumar Wase, Inusa Jarmai yace ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu fiye da dari biyar sun kuma sace mutane a ranar Jumma’a.

Shima kansila mai wakiltar Gimbi da Pinau a karamar hukumar Wase, Adam Umar yace ‘yan bindiga sun kori manoma da makiyaya dake rayuwa a kauyukan yankin da dama.

Kakakin rundunar dake samar da zaman lafiya a Jahar Filato, Manjo Ishaku Takwa a sakon kar-ta-kwana ya shaida wa muryar Amurka cewa ‘’Wase na can, hankali kwance’’.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

'YAN BINDIGA SUN MAMAYE KAUYUKAN WASE DA KANAM A JAHAR FILATO OK.mp3