SOKOTO, NIGERIA - Bayan harin da yayi sanadin salwantar rayukan jama'a fiye da talatin a garin Tangaza da ke jihar Sokoto, an samu rahotannin sake kai hare-hare a wasu yankuna da suka hada da Gwadabawa, Wurno, da Isa duk a gabashin jihar Sokoto.
Harin da ya dauki hankalin jama'a shi ne wanda aka kai wa wasu al'ummomi da ke karamar hukumar Illela, mai makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, wanda ya dakatar da zirga-zirga a kan titunan Sokoto zuwa Illela, kuma ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.
Wani mutumin Illela ya ce lamarin ya soma ne a lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a garin Tozai inda suka kashe mace daya, daga nan suka wuce zuwa garin Garu, a nan kuma suka tattara dabbobi masu yawa suka wuce da su.
Muhammad Ibrahim Garu, mazaunin garin Garu ne, ya ce ‘yan bindigar sun kashe mutum takwas a ranar farko, washe gari kuma suka tsinci gawar mutum biyu.
Sai dai daga baya 'yan bindigar basu ji da dadi ba, sakamakon musayar wutar hadin gwiwar jami'an tsaro da ta sa har suka samu nasarar kama mutum biyar, duk da cewa sun yi barna a garin na Garu a cewar wani mazaunin Illela.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya a ta bakin mukaddashin kakakinta a Sokoto Ahmad Rufa'i, ta tabbatar da aukuwar lamarin tana mai cewa barayin sun shiga garin Garu su da yawa sun kuma kore dabbobin jama'a.
Rufa'i ya ce bayan da jama'ar garin suka bi su sun yi musu kwaton bauna har suka kashe mutum hudu, amma jami'an tsaro sun kai musu daukin gaggawa har suka kama 'yan bindiga shida da babura biyu.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da sabuwar gwamnatin jihar Sokoto ta ce zata yi duk mai yuwa wajen kawar da ayyukkan ‘yan bindiga inda har ta fara bincike a kan matsalolin da ke kawo cikas wajen yaki da ‘yan bindiga, da zummar magance su.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto Abubakar Bawa, ya ce bayan shirin su na karfafa gwiwar jami'an tsaro da ke fagen daga, za su yi amfani da jami'an tsaron banga su yi aiki tare da jami'an hukuma.
Yanzu dai babbar fatar jama'ar jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara da sauran yankunan da ke fama da rashin tsaro ita ce ganin an samu mafita ga wadannan matsalolin da ke kawo tarnaki ga jama'a da hana ci gaban yankunan.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5