Wasu ‘yan bindiga sun kashe Manjo-Janar Hussein Ahmed, wanda darekta ne a hedkwatar sojojin kasa na Najeriya.
Wasu rahotannin sun ce maharan sun kuma yi garkuwa da matarsa wacce suke tare da ita a lokacin harin.
Janar Ahmed na kan hanyar komawa Abuja ne daga Okene a lokacin da maharan suka budewa motarsu wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Wata sanarwa da darektan yada labaran sojojin Najeriya Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta tabbatar da aukuwar lamarin, a cewar jaridun Najeriya.
“Wannan abin alhini ya faru ne yayin da ‘yan bindiga suka kai hari kan motar babban sojan a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga Okene da ke jihar Kogi a ranar 15 ga watan Yulin 2021.” Jaridun Najeriya da dama suka ruwaito sanarwar da Janar Nwachukwu ya fitar.
Karin bayani akan: Manjo-Janar Hussein Ahmed, Onyema Nwachukwu, Laftnar-Janar Faruk Yahaya, ‘yan bindiga, sojojin, Nigeria, da Najeriya.
Sai dai sanarwar ba ta ce komai ba game da rahotanni da ke cewa an yi garkuwa da mai dakin Janar Ahmad.
Rahotannin har ila yau sun yi nuni da cewa a kwanan nan babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftnar-Janar Faruk Yahaya ya nada marigayin a matsayin darekta a hedkwatar sojin kasar da ke Abuja.
Matsalar ‘yan bindiga da ke satar mutane don neman kudin fansa ta jima tana addabar Najeriya, lamarin da ya kan yawan rutsa da matafiya da har ma da dalibai da ke makarantu.