Su dai sojojin suna aikin sintiri ne da ya kunshi wani hafsa daya da sojoji goma da aka ba da labarin sun bace bat, al'amarin da yasa aka aika da karin dakarun rundunar Operation Whirl Strike don neman su.
Kakakin hedikwatar sojojin Najeriya, Brigediya Janar Mohemmed Yerima, ya ce daga bisani an gano gawarwakin baki dayan sojojin a karamar hukumar Konshisha da ke jihar ta Benue.
Rundunar sojojin Najeriyar ta ce tuni dai an debe gawarwakin sojojin, kuma an kaddamar da farautar 'yan bindigar da suka tafka wannan aika-aika dan gurfanar da su gaban kotu.
Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da samar da cikakken zaman lafiya a jihar Benue da ma sauran sassan Najeriya.
Jihar Benue dai na daya daga cikin jihohin Najeriya dasuka fi fuskantar tabarbarewar tsaro a Najeriya, don a baya ma gwamnan jihar ya fuskaci wani hari yayin da yake gonarsa.
Saurare cikakken rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5