Bayanai daga yankin da wannan al’amari ya faru sun yi nuni da cewa, a dai dai lokacin da mazaunan kauyen Gaigorou dake kusa da iyakar Mali ke jana’izar wani mamaci a ranar asabar din da ta gabata ne ‘yan bindiga suka zo akan gomman babura dauke da bindigogi suka kuma bude wuta akan wadanan bayun Allah abinda ya yi sanadin fararen hula a kalla 19.
Masu fashin baki akan sha’anin tsaro irinsu Alkassoum Abdourahamane na ganin faruwar wannan al’amari a cikin watan Ramadan wani abu ne da ke nunin ba wata alaka a tsakanin ayyukan ta’addanci da dalilan addinai.
Dubban sojojin cikin gida da na kasashen waje ne ke jibge a yankin da kasashen Nijer da Mali da Burkina Faso ke makwaftaka da sunan yaki da ta’addanci yayinda gwamnatocin wadanan kasashe suka haramta amfani da babura dalili kenan jama’a ke mamaki yadda ayarin ‘yan bindiga ke watayawa hankali kwance.
A jiya lahdi ministan cikin gida Alkache Alhada da gwamnan jihar Tilabery Tidjani Ibrahim Katchiella sun ziyarci kauyen na Gaigorou domin jajantawa jama’a game da faruwar wannan al’amari. Suna masu jaddada daukan matakan samarda tsaro.
Kisan fararen hula wani sabon salo ne da ‘yan bindiga suka bullo da shi a ‘yan makwanin nan a jamhuriyar Nijer. A watan jiya irin haka ta faru a gundumar Tilia ta jihar Tahoua inda ‘yan taadda suka hallaka mutane 137 kwanaki kadan bayan kisan wasu fatake 58 a gundumar banibangou dake jihar Tilabery duk kuwa da cewa yankuna ne da hukumomin Nijer suka aiyana dokar ta baci.
Saurare cikakken rahaton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5