'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 7 Suka Kuma Yi Garkuwa da Wasu 100 A Katsina

Yan bindiga a jihar Sokoto

Akalla mutane bakwai ne aka kashe tare da yin garkuwa da 100 a daren Asabar bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Mazauna kauyukan da kuma 'yan sanda sun ce, wasu gungun ‘yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare kan al’ummomin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, inda suke yin garkuwa da jama’a da dalibai da masu ababen hawa domin neman kudin fansa.

Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar da ke kan babura sun isa kauyen Maidabino da ke karamar hukumar Danmusa a Katsina, inda suka fara harbe-harbe da dai suka isa kauyen, lamarin da ya tilastawa mazauna kauyen tserewa.

'Yan bindiga sun tada garuruwa

Hassan Aliyu ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho cewa, harin ya baiwa mazauna yankin mamaki kuma an tabbatar da bacewar wasu mata da yara da dama. Ya ce, “Sun kashe mutane bakwai ciki har da yara biyu da suka kona. Sun kwashe sama da sa'o'i shida suna lalata mana kadarori."

A nasa bayanin, Auwalu Ismail, wani mazaunin garin ya ce ‘yan bindigar sun fara tare dukkan hanyoyin da ke zuwa Maidabino kafin su kai harin. Ya ce, “Sun kona shaguna da ababen hawa, sun kwashe mana dabbobi, sun kuma yi garkuwa da mata ta, da wadansu mata da yara sama da 100."

'Yan bindiga a yankin jihar Kebbi

Muhammad Sani, wanda aka sace ‘yar uwar sa ya bayyana cewa, “Sauran mutanen da ba su gudu ba, suna rayuwa ne cikin tsoro... kuma suna jiran jin labarin ‘yan uwansu da aka sace.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Abubakar Aliyu Sadiq ya tabbatar da faruwar harin da kuma mutuwar mutane bakwai amma bai iya bayyana ko akwai wanda ya bata ba. Sai dai ya bayyana cewa, ‘yan sanda na gudanar da bincike.

Ku Duba Wannan Ma ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 50 A Wani Sabon Hari A Katsina