Wannan na zuwa ne yayin da a ranar Lahadi ‘yan bindiga suka hallaka kwamandan yanki na jami'an Mopol tare da jami'an sa biyar da mutanen gari kimanin talatin a jihar Kebbi.
Murnar da jama'a suka soma a wasu yankunan arewacin Najeriya akan samun saukin matsalar rashin tsaro ta fara komawa ciki, domin matsalar na son sake tanyacewa a yankunan.
A jihar Kebbi da ke arewa maso yamma, yankin ‘yan bindiga sun sake baje hajarsu a wasu yankunan kudancin jihar, inda suka hallaka mutane fiye da talatin ciki har da jami'an ‘yan sandan kwantar da tarzoma shida.
Wani jami'in tsaro na sa-kai, wanda baya so a ambaci sunansa saboda dalilin tsaro, ya bayyana cewa tun ranar Asabar da dare suka samu labarin cewa, barayi sun fito daga yankin ‘Yar Maitaba zuwa Jambali zuwa Mai Rairai har zuwa Dan Umaru cikin yankin Danko Wasagu kuma nan take suka hadu da jami'an Banga da Mopol karkashin jagorancin kumandan yankin na Mopol suka je kai dauki.
Ya ce sun yi tafiya kusan kilo mita daya suna tafiya sai suka ci karo da baburan barayin kimanin 210 sun nufaci hanyar garin Dadin Duniya, daga nan barayin suka kewayo suka zagaye su, nan ne suka yi dauki-ba-dadi da barayin har Allah ya yi wa kwamandan yanki na Mopol Ibrahim Idris Sakaba da wasu jami'an sa rasuwa, kuma duka mutane 34 ne suka rasa rayukansu a lokacin harin.
Harwayau wani mutumin garin Dan Umaru wanda yana cikin garin aka kai harin, Alhaji Sani Bawan Allah, ya,ce gaban Idonsa barayin da suka kai harin sun wuce babur 200, kuma sun kira jami'an tsaro na Soji ba su zo cikin lokaci ba, jajirtaccen kwamandan mopol na Bena ne ya je kai musu dauki, inda Allah ya yi masa cikawa shi da jami'an sa, da wasu mutane fiye da talatin.
Wannan lamarin dai ya girgiza jama'ar yankin musamman na garin Bena, inda nan ne kadai mafaka ta jama'ar yankunan,
Wani mutumin garin Salihu Muhammad Bena ya jaddada kira ga mahukunta akan su rika baiwa tsaron yankunan muhimmanci.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto duk kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda akan lamarin ya ci tura inda na kasa samun kakakin rundunar a jihar Kebbi SP Nafi’u Abubakar, da farko na kira layin sa yana rufe daga baya kuma an bude layin amma bai dauki kira ba.
Amma wani jami'in tsaron sa-kai da aka fafata da shi a lokacin harin ya ce yana son duniya ta sani cewa Kwamandan Mopol da aka kashe shi kadai ne suke samun karsashi da aikin sa, kuma shi ne kadai jami'in tsaro da ke taimakawa jami'an tsaro na sa-kai, don haka yanzu ba su san yadda lamarin zai kasance ga jama'ar yankin ba.
Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da hana jama'a bacci da idanu biyu rufe a wasu yankunan Najeriya domin ko a yankin Shinkafi ta jihar Zamfara, ‘yan bindiga sun yiwa wasu kisan gilla a ranar Asabar da ta wuce, duk da yake mahukunta na kokarin shawo kan matsalolin.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5