'Yan Bindiga Sun Kashe Kananan Yara a Wani Hari Da Suka Kai Wata Makaranta A Kamaru

'Yan sanda kwantar da tarzoma a Kamaru

Wasu mutane rike da makamai sun kai hari kan wata makaranta dake garin Kumba a kudu maso yammacin Kamaru, inda suka kashe akalla yara 4 kuma suka raunata wasu 15. 

(

Asabar din nan wasu mutane rike da makamai suka kai har kan wata makaranta da ke garin Kumba a kudu maso yammacin Kamaru, inda suka kashe akalla yara 4 kuma suka raunata wasu 15.

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin wannan hari amma gwamnati ta alakanta lamarin ga ‘yan aware da ke kira ga gwamnati da a rufe makarantun yankin.

Wani dan shekaru 17, Patrick Ebale yace, har yanzu bai farfado daga faduwar gaba da ya shiga ba sanadiyar faruwar lamarin na ran asabar, da ‘yan bindiga suka kai hari makarantar da ake kira Mother Francis International Bilingual Academy dake Kumba.

Wani dalibi da Muryar Amurka ta yi hira da shi ya bayyana cewa “An shiga rudani a kewaye sai da na shiga cikin kwata na buya cikin mazurarar ruwa domin na kare kaina kada harsashi ya same ni. Mun fito ne daga cikin al’umman da kowa ya san kowa kuma wadanda suka kai mana hari, mutane ne da muke hulda dasu. Saboda haka zuwa makaranta ba abu mai sauki bane.”

Babban jami’in gwamnati a bangaren gudanarwa na Meme, inda Kumba take, Chamberlin Ntouou Ndong, yace yara 4 ne aka kashe nan take. Ya kuma ce 7 daga cikin wadanda suka samu raunuka na cikin mawuyacin hali.

Ndong yace, ‘yan aware na fada ne da kan kirkiro jiha mai amfani da harshen ingilishi da suke kiran kansu Ambazonia, kuma suke da alhakin wannan Karin da kashe- kashen.

“Bari na yi amfani da wannan damar ba don kawai in yi Allah wadai da wannan abunda ya faru ba, ina so in jaddada cewa za muyi kokarinmu. Su yi ta gudu, muna bayansu. Bari in kuma yi amfani da wannan damar in gayawa iyaye. Ban ga dalilin da wadannan ‘yan Amba zasu kai wa yara hari da rana tsaka ba, kuma mutanen da ke kewaye suna kallo basu kai musu dauki ba.”

Babu wanda ya fito ya dauki alhakin wannan hari, amma a watan Satumba, wasu mayakan ‘yan awaren sun yi gargadi akan kada a bude makarantun Kamaru da suke bangaren da ke amfani da harshen Ingilishi. Mayakan sun ce ba zasu iya ba yara kariya ba a makarantu kuma suka umurci gwamnatin tsakiya a Yaounde da su janye sojoji idan suna son bude makarantu.

Mafi yawan makarantun Areawa Maso Yammacin Kamaru sun kasance a rufe tun shekaru 4 da aka fara fada domin kirkiro jihar masu amfani da harshen Ingilishi daga Kamaru da mafiya rinjayan masu harshen faranshi.

An bude makarantu a fadin Kamaru ranar 5 ga watan Oktoba bayan an shafe watanni 6 ana hutun da COVID-19 ya tilasta rufe makarantu. Gwamnati tace yaran masu amfani da harshen Ingilishi dubu 30,000 ne suka koma makaranta duk da barazanar tashin hankalin.