Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Sojoji Da ‘Yan Sanda Da Hannu a Bacewar Dalibai 43 a Mexico


Hukomomi a kasar Mexico sun bayar da sammacin kame sama da dozin kan ‘yan sanda da sojojin da aka yi imanin suna da hannu a bacewar daliban kwaleji 43 a shekarar 2014, a cewar jagoran binciken ranar Asabar.

Omar Gomez, shine shugaban masu binciken ya fadi a wani taron manema labarai a birnin Mexico City cewa, an samar da sammacin ne kan wadanda ke da hannu da wanda suka shirya, ciki har da sojoji da ‘yan sandan jiha da na tarayya.

Sanarwar na zuwa ne lokacin bikin cika shekaru shida da yin garkuwa da daliban. A wurin taron, akwai shugaban kasar Mexico Andres Manuel Lopez da shugaban hukumar kare hakkin bil Adama, Alejandro Encinas, sai kuma ‘yan uwan daliban wadanda suka halarci taron dauke da hotunan daliban da suka bace.

Ranar Asabar itace ranar farko da hukumomin Mexico suka sanar da an bayar da sammacin kama sojoji. Tun farkon mako ne kamfanin dillancin labaru na Reuters ya rawaito cewa sammacin da aka fitar abu ne sananne.

Batun bacewar daliban da matasa ne maza wadanda ake yiwa horon zama malaman makaranta a kasar, ya haddasa gagarumar zanga-zanga a 2014 ya kuma janyo Allah wadai daga kasashen duniya, ya zamanto missali na rashin daukar matakin gwamnati wajen kare tashin hankali tare da hukunta masu laifi.

A watan Yuni, hukumomi sun sanar da kama shugaban ‘yan dabar Guerrero, wanda aka zarga da hannu a bacewar daliban da kuma sammacin kama wasu ‘yan kungiyar dake da alaka da wannan danyen aiki.

Iyalai daliban sun dade suna zargin hukumomin Mexico, ciki har da sojoji da hannu a bacewar matasan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG