Wani dan yankin da abin ya faru a idonsa ya shaida wa Muryar Amurka tare da alkawarin ba za a ambaci sunansa ba cewa da misalin karfe sha biyu da rabi ne ‘yanbindiga suka kawo musu harin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 6 a yankin nasu.
Malan Zakari Adamu Masin wani mazaunin wannan yankin, ya ce ‘yan bindiga sun dade su na addabarsu a kauye tare da yin lalata da ‘yayansu.
Bala Bobbo Gomna, haifaffen kauyen Kararr ne a karamar hukumar Gasol a jihar Taraba ya kuma tabbartar da cewa 'yan bindigar sun dade suna cin karensu ba babbaka a kauyen da yin garkuwa da mutane domin kudin fansa.
Ardo Kiri da ke zama shugaban Sullubawa na karamar hukumar Gasol ya ce a yanzu haka dai su na mawuyacin hali domin ba su da tudun dafawa rana zafi inuwa kuna.
A nasu bangaren jami’an ‘yansanda na jihar Taraba ta bakin kakakin rundunar, DSP Usman Abdullah, ya ce sun hada runduna ta hadin gwiwa domin ganin an kawo karshen ‘yan bindigan a jihar Taraba baki daya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5