'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Karamar Hukumar Ikorodu Dake Jihar Lagos

Wani Bangaren jihar Lagos

Wasu yan bindiga da har yanzu ba a san kosu wanene ba, sun kai hari wani kauye da ake kira Elegbede dake yankin karamar hukumar Ikorodu dake jihar Lagos. Rahotanni daga yankin na cewa anyi bata kashi tsakanin yan bindigar da kuma jami’an yan sandan jihar Lagos.

A cewar kakakin rundunar Yan Sandan jihar Lagos, SP Dolabo Badmos, babu kamshin gaskiya game da rahotannin da ake bazawa cewa an kashe mutane 13 a wannan hari. Kawo yanzu dai ba a san ko su wanene ba suka kai harin, sai dai wata majiya ta sheda cewar maharan yan yankin Niger Delta ne dake kai hare hare akan bututan Man fetur a wannan yanki.

Kwanaki hudu da suka gabata ma dai yan bindigar sun kai makamancin wannan hari a karamar hukumar Shagamu ta jihar Ogun, inda suka kashe mutane da dama a wannan yanki dake makwabtaka da juna na gaban ruwan jihohin guda biyu.

Wani dake zaune a yankin na Ikorodu wanda kuma baya son a anbaci sunansa ya shaidawa wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibrin, cewa babu mutuwa a wannan hari sai dai mutane da dama sun samu rauni, kuma yan sanda sun kama wasu daga cikin maharan.

Duk da yake kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan Lagos yaci tura, wani kwamandan yan sandan kwantar da tarzoma dake yankin ya fadi cewar sun shawo kan lamarin. Sai dai har yanzu mutane na ta kaura daga yankin.

Hare haren yan bindiga a wannan yanki ba sabon abu bane daga yan yankin na Naija Delta wadanda ke kai hare hare a bututan Man fetur daya taso da yankin Naija Delta zuwa tashan jiragen Ruwan Lagos.

Your browser doesn’t support HTML5

'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Karamar Hukumar Ikorodu Dake Jihar Lagos - 2'11"