Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sabon Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda A Najeriya


Yan Sandan Najeriya
Yan Sandan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Kpotun Idris a matsayin sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Shi dai Ibrahim Kpotun Idris, ‘dan asalin garin Kutigi ne dake karamar hukumar lavun ta Jihar Neja. An haifeshi ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1959.

Ya fara aiki da rundunar ‘yan sandan Najeriya a shekara ta 1984, bayan da ya kammala karutunsa a jami’ar Ahmadu Bello Dake Zariya.

Idris ya rike mukamai da dama a rundunar ‘yan sandan Najeriya, ciki harda rike mukamin Kwamandan ‘yan sandan kwantar da tarzoma wata mobile na tsawon shekaru 17. Ya rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda a jihohin Nasarawa da Kano.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG