‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Bututun Mai Tsakanin Nijar Da Benin

Bututun Mai

Wasu ‘yan bindiga da ke adawa da Gwamnatin mulkin Nijar sun tarwatsa wani bangaren bututun man kasar da China ke marawa baya a wani hari da su ka kai a ranar Lahadi da dare

Bututun man mai daukar ganga 90,000 a kowace rana na da tazarar kusan kilomita 2,000 (mil 1,243) wanda ya hada rijiyoyin mai na Agadem na Nijar da gabar tekun Benin.

Ana kyautata zaton fitar da kayayyakin da aka sarrafa zuwa kasashen ketare karkashin wata yarjejeniyar dala miliyan 400 da kamfanin mai na kasar China wato National Petroleum Corp (CNPC).

Jam'iyyar Patriotic Liberation Front (FPL) ta ce harin da ta kai kan bututun man na da nufin ingiza China ta soke yarjejeniyar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. An kafa FPL ne bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a watan Yulin 2023.

"Idan hakan bai yiyu ba, duk kadarorin mai za su gurgunce a wasu ayyuka masu zuwa," in ji FPL.

Gwamnatin Nijar, da Petro China, da CNPC, da kamfanin bututun mai na Afirka ta Yamma (WEPCO) ba su amsa bukatar jin ta bakinsu akan harin ba.

Harin ya kara dagula rikicin da ya dabaibaye kafa bututun man din, wanda Nijar, a ranar Alhamis da ta gabata, ta ce ta rufe saboda rikicin iyaka da kasar Benin.

Hakan ya zo ne kwana guda bayan wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari kan sojoji da ke gadin bututun mai a yankin kudu maso gabashin Dosso. Sojoji shida ne suka mutu, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

-Reuters