'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Ziarat Kasar Pakistan

'Yan bindiga sun kai hari a yau Laraba a wani sansanin tsaro a kudu maso yammacin Pakistan, inda suka kashe akalla dakarun soji shida.

An kai hare-haren a Ziarat, wani kebabben sashi, a yankin Baluchistan wanda shine mafi girma mai tattare da albarkatun kasar.

Qadir Bakhsh Pirkani, Mataimakin kwamishinan Ziarat, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, jami'an tsaro sun kaddamar da bincike a yankin don kokarin kama 'yan ta'addan da suka kai hare hare, kimanin kilomita 50 daga babban birnin lardin Quetta.

Haramtacciyar kungiyar Tehrank-e-Taliban Pakistan (TTP) da aka fi sani da Pakistan Taliban, ta dauki alhakin kai hare-haren.

Wani kakakin mai magana da yawun TTP, ya fada a wata sanarwa cewa, an kai hare-hare ne a matsayin ramuwr gayya kan kisan da dakarun tsaro da aka tura yankin suka yiwa wadansu mambobinsa.