Wani babban jami’i a gwamnatin Trump ya fadawa manema labarai tun kafin ziyarar Bolsonaro, yana mai cewa kasashen biyu suna da muhimman batutuwa da zasu tattauna a kan noma kuma shugabannin biyu zasu sanar da sakamakon tattaunawar a wata sanarwar hadin gwiwa a yau Talata.
Wasu abubuwa da zasu kuma tattauna akai sun hada ne da batun kawo ‘yan kasuwar Brazil da na Amurka kusa da juna da kuma batun kulla huldar makamashi da ta gine gine.
Babban jami’in gwamnatin Amurkan yace kasashen biyu zasu hada kai wurin taimakawa shugaban Venezuela Juan Guaido, wanda kasashen yammacin duniya har da Amurka suke daukar shi shugaban kasar Venezuela na gaskiya.
Facebook Forum