‘Yan sanda sun ce an kammala gwaji a kan gawarwakin, amma 12 kadai a cikin su ne aka iya gano su a hukumance, a cikin wannan rukunin an riga an bada guda shida ga iyalansu.
Wata sanarwar da ‘yan sandan Christchurch suka fitar a yau Talata na cewa, duk da yake za a iya ganin tantance gawarwakin abu ne mai sauki, amma yana da matukar sarkakiya , musamman a cikin wannan hali. Ba a bayyana sunayen wadanda harin ya rutsa dasu ba, ko da yake an bada sunaye na farko ga iyalansu.
Tsawon lokacin da aka jira ya kara nawaitawa iyalai masu makoki, wadanda suke kokarin ganin sun yi jana'izar masoyansu. Addinin Musulunci ya bukaci a gaggauta wankewa da kuma sutura gawa nan da nan, idan ya yiwu cikin sa’o’I 24 da rasuwa.
Facebook Forum