Mahara dauke da manyan bindigogi sun hallaka mutane 3 da ya hada da yarinya 'yar kimanin shekaru 6, a jihar Neja a Najeriya.
Rahotanni daga yankin Kotonkoro na karamar Hukumar Mariga sun nuna cewa 'yan bindigar sun yi ta harbin motocin jama'a a daidai lokacin da matafiya ke kan hanyarsu ta shiga kasuwar garin.
Wani Mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, 'yan bindigar sun yi awon gaba da mutane da dama, ciki har da masu aiki a gonakinsu na shinkafa.
Wani mazaunin yankin, Alhaji Shehu Kotonkora ya ce, an kashe wani direba da ke tuka motarsa a lokacin da wadannan mahara suka kai wannan hari.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin dai babu wani karin haske da aka samu daga rundunar 'yan sandan jihar Neja akan lamarin, domin kuwa kokarin samun kakakin 'yan sandan jihar, Wasi’u Abiodun ta wayar salula ya ci tura,
Amma shugaban karamar Hukumar ta Mariga Hon. Abbas Kasuwar Garba ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce 'yan bindigar sun fito ne daga dajin Zamfara, kasancewar yankin na da iyaka da wannan daji da ya hada jihohin Zamfara da Kebbi da kuma dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Wannan hari dai ya jefa dubban jama'a musamman manoma cikin yanayi na fargaba ganin yadda ake kokarin cire amfanin gonaki.