'Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 6, Sun Sace 13 A Jihar Zamfara

Motar Sulke Da Yan Bindiga suka kona a Zamfara.

Motar Sulke Da Yan Bindiga suka kona a Zamfara.

Wasu yan bindiga sun aukawa garin Dan Sadau da ke jihar Zamfara da safiyar yau juma’a inda suka kashe wasu mutane hudu tare da yin awon gaba da wasu mutane 13 ciki har da matan aure hudu.

A cikin mutane hudu da yan bindigan suka halaka, uku daga cikin su raunin harbin bindiga ya yi sanadiya mutuwarsu inda yan bindigan suka yiwa dayan matashin yankan rago.

Haka kuma, ‘yan bindigan sun aukawa wata motar yakin sulke da ke kan hanyar zuwa kai dauki a garin na Dan Sadau da harbin bindiga kana suka kona motar, saidai matukin motar yakin ya sami tsira da ransa a yayin harin.

Motar Sulke Da Yan Bindiga suka kona a Zamfara.

Motar Sulke Da Yan Bindiga suka kona a Zamfara.

Wakilinmu a jihar ta Zamfara ya tabbatar mana da labarin hakan ne bayan halartar jana’izar mutane 4 da suka rasa ransu sakamakon harin na yan bindigar, da misalin karfe 10 da rabi na safiyar yau juma’a.

Mahukunta daga jihar ta Zamfara ma sun tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilinmu, inda suka ce an fara aikin ceto mutanen da yan bindigan suka yi awon gaba da su.

A halin yanzu dai jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda sun isa wurin motar sulke da yan bindigan suka kona don janye ta daga kan hanya.