‘Yan Bindiga Sun Fara Kai Hare-Hare Wasu Sabbin Yankunan Jihar Sokoto

‘Yan Bindiga

Matsalolin rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da mamaye sassan kasar, suna ta illata yankunan arewa da jama'ar yankin.

SOKOTO, NIGERIA - Abinda ke nuna hakan shine yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da fadada ayyukan su zuwa wasu sababbin yankuna da ba'a tunanin ayyukan su kai wurin kamar abinda ke faruwa yanzu a wasu yankuna na arewa maso yammacin Najeriya.

A can baya akwai wasu yankunan Najeriya da suka yi kaurin suna akan ayyukan 'yan bindiga inda suka kafa sansanoni suna cin zarafin jama'a, alal misali kamar yankin gabascin Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya.

Duk da yake har yanzu ‘yan bindigar na ci gaba da tafka ta'asar su a wasu daga cikin wadannan yankunan, haka ma suna fadada ayyukan zuwa wasu sababbin wurare.

Yankin Durbawa dake cikin karamar hukumar Kware wadda daga ita sai kwaryar birnin Sakkwato ya soma daukar bakuncin ‘yan fashin daji inda jama'ar garin suka soma kokawa.

‘Yan Bindiga

Uban kasar yankin Mu'azu Yakubu Durbawa ya nuna damuwa akan idan ba'a yi saurin kawo daukin magance matsalar ba to fa ba'a san adadin illolin da zata haifar ba.

Yankin Girabshi dake karamar hukumar Wamakko cikin garin Sakkwato shima yana fuskantar hare-haren barayi dake shiga gida-gida suna addabar jama'a.

Sau da yawa jami'an tsaro ke cewa suna kan kokarin su na magance matsalolin da samar da tsaron rayukan jama'a, amma kuma matsalolin na ci gaba da wanzuwa abinda masharhanta kamar Farfesa Bello Badah ke cewa da ana samun hadin kan mahukumta ga tunkarar wannan matsalar tamkar yadda suke hada kai a fagen siyasa, da watakila zuwa yanzu matsalar ta zama tarihi.

‘Yan Najeriya dai na cike da fatar ganin lokacin da za'a samu fita daga wadannan musifu ko da talaka zai samu saukin rayuwa.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

‘Yan Bindiga Sun Fara Kai Hare-Hare Zuwa Wasu Sabbin Yankunan A Jihar Sokoto