Da aka tuntubi rundunar ‘Yan-sandan jihar Zamfara akan wannan batu, Kakakinta DSP Shehu Muhammad ya ce zai bincika.
WASHINGTON D.C. —
Ana ci gaba da samun tabarbarewar tsaro a Arewancin Najeriya inda abubuwa ke kara fitowa fili cewa, ‘yan bindiga-dadi ke gudanar da ikon wasu yankunan karkara da ke jihohin Arewa maso Yammacin kasar.
“Yanzu haka akwai wani dan fashi da makami wanda ita gwamnati ta yi sulhu da shi kuma ana tsammanin ya yarda da sulhun, amma yana ta yi wa jama’a bi-ta-da-kulli. Sunansa Hassan Bamamu. Yanzu haka ya je kasar Bawa-Ganga ya tara kauyuka guda bakwai. Ya sanya musu kudin fansa, su kawo miliyan talatin da bakwai” a cewar wani mazaunin yankin.
Dalilin hakan ya sa wadannan mutane suke neman gwamnatin Najeriya ta tsare rayuwarsu, kafin ‘yan bindiga su kashe su gaba daya.
“Muna roko, dan Allah ga Janaral Mungunu, Mai ba Shugaban Kasa shawara akan harkar tsaro, da Janaral Faruk Yahaya, Shugaban Sojoji na kasa, su taimaka mana, su yi wa Allah da Annabi, su kawo mana dauki kafin wannan lokaci da wadannan mutane miyagu suka sa mana, domin jama’armu ba su da wannan kudade.”
Mutanen kauyukan sun shaida cewa sun kai koken su a hukumance ga Mai Martaba Sarkin Tsafe da Babban Baturen ‘yan sanda yanki wato DPO, da ma gwamnatin Jihar Zamfara. To amma sun ce suna farbagar kamar ba za a iya tsare rayuwar nasu ba.
Da aka tuntubi rundunar ‘Yan-sandan jihar Zamfara akan wannan batu, Kakakinta DSP Shehu Muhammad ya ce zai bincika.
Hukumomin Najeriya dai suna ci gaba da cewa suna iya bakin kokarin a yakin da suke yi da 'yan fashin daji don ganin sun yi galaba akansu.
Saurari rahoton cikin sauti:
‘Yan bindiga Na Ci Gaba Da Yankawa Wasu Kauyukan Zamfara Harajin Miliyoyin Nairori - 3'01