Mai magana da yawun wannan ayari dake bayyana wannan koke shine Alhaji Muhammadu Gaskanta yace tun lokacin da demokradiyya ta koma Najeriya a 1999, shiyya ta 1 da ta 2 ne ke bada gwamna da mataimaki, amma shiyyarsu ta uku basu taba samun wannan gata ba.
“Abunda yake tafe da mu, albishir ne mai kyau. Da farko mun nemi alfarmar a bar mana wannan takara kamar yadda aka yi shekara 16. Wannan shugabanci na Jihar Yobe, tsakanin Zone A da Zone B yake zuwa. Mu zone C bamu taba yi ba” a cewar Alhaji Gaskanta.
Mr. Gaskanta ya kara da cewa an hanna mutan ‘yankinshi siyar takardar tsayawa takara, inda yace zasu dauki mataki akan hakan.
“Wannan maganganu da mukeyi na daga cikin abunda zai jawo hankulan jama’a su fahimci irin matsalar mu.”
Alhaji Muhammadu Gaskanta ya nemi hadin kan jama’a domin su mara wa ‘yan yankinshi baya wajen samun izinin tsayawa takarar gwamna a shekara ta 2015.
Your browser doesn’t support HTML5