A yau Laraba ne Bankin Raya Afirka ta AfDB ya ce kimanin mutane miliyan 600 a nahiyar Afirka ke fuskantar kalubalen rashin wutar lantarki.
Bankin ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Hukumar dake kula da samar da wutan lantarki a karkara ta Najeriya ta shirya da hadin gwiwar kungiyar tarayyar Turai ta EU a Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.
Ajandar taron shi ne ta yaya za a iya zuba hannun jarin samar da makamashi a Afirka?
Taron ya kuma samu wakilcin kwararru da dama daga kasashen duniya daban daban da suka hada da masu zuba jari da na gwamnati, da wakilan masana’antu, domin tattauna hanyoyin zuba jari a fannin samar da wutar lantarki mara gurbata muhalli a Afrika.
Malam Abba Abubakar Aliyu shine mukaddashin shugaban hukumar samar da hasken wutan lantarki a Najeriya wanda yayi karin haske game da kokarin da hukumar sa ke yi na samar da haskin wutan lantarki domin raya karkara, wanda ya ce hukumarsa na iya kokarinta wajen samar da hasken lantarki na makamashi irin na solar domin inganta harkokin noma a yankunan karkara.
A bangaren ta Madam Eloeige Herz na kungiyar sa kai na ADA da ke Luxembourg ta ce yanzu haka "muna aiki a wasu kasashe na yanmacin Afirka irin su Senegal, Benin da Birkina faso da Mali, kuma kokarin mu shine fara aikin samar da solar mai inganci a Najeriya bisa la'akari da mahinmamcin sa wajen raya kasa".
A cewar Bankin Raya Afirka (AfDB), akalla 'yan Afirka miliyan 600 har yanzu ba su da wutar lantarki, ciki kuwa harda Najeriya, inda har yanzu mutane miliyan 90 ba su da wutar lantarki.
A wani bangare na shirin samar da wutar lantarki a Najeriya (NEP) wanda Bankin Duniya ke daukar nauyinsa, REA na bayar da tallafin da ya dace ga kananan kamfanoni masu fafutukar neman mukamashi a yankunan karkara.
Saurari rahoton Babangida Jibrin:
Your browser doesn’t support HTML5