A baya gwamnan jahar birnin Yamai, ya haramtawa ‘yan adawan kasar gudanar da wannan gangami, amma a wannan karo ‘yan adawan sun ce ko da izni ko ba iznin hukumomi ba za su fasa yin jerin gwanon ba.
Dauda Kankama, na daga cikin mambobi na kawancen na ‘yan adawa, ya kuma ce ba a ban ka’idaji wajen shirye shiryen zaben.
“Wannan rijista da aka yi ta ‘yan kasa, yawancin ‘yan kasa ba su amince da ita ba saboda ba a yi aiki bisa ka’ida ba da kuma abinda ‘yan kasa ke so ba.” In ji Kankama.
A cewarsa, “ranar Lahadi mai zuwa na daya ga watan Nuwamba, muna kira ga ‘yan kasa, mutanen birnin Yamai, ranar nan za mu fito kwanmu da kwarkwatanmu.”
Kankama ya kara jaddada cewa idan suka nemi izni kamar su nema ne a basu, “babu wnai izni, doka ta amince a bamu, idan suna so su bamu jami’an tsaro, babu inda doka ta ce a je a tambaya.”
A shekara mai zuwa jamhuriyar ta Nijar ke shirin gudanar da zaben ta n agama gari.
Domin jin karin bayani kan wannan rahoto ga rahoton da wakilin Muryar Amurka, Yousef Abdoulaye ya hada mana:
Your browser doesn’t support HTML5