Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Tashin Boma Bomai a Jamhuriyar Nijar


Boko Haram
Boko Haram

Wannan harin ya faru ne da asubayi ya’u yayin da kuma jiya ne sabon Gwamnan jahar Diffa Abdu Kaza ya fara aiki

An samu tashin Boma Bomai a Bulanguri dake kusa da Diffa, wasu yen kunar bakin wake ne suka kai inda yayi sanadiyar rasuwar Sojoji biyu yayin da uku suka jikkata.

Wannan harin ya faru ne da asubayi ya’u yayin da kuma jiya ne sabon Gwamnan jahar Diffa, Abdu Kaza ya fara aiki, haka kuma gobe ne
shugaban kasa Mahamadu Isufu zai kai ziyara Agadem inda ake hako da
mai dake yankin na Diffa.

Wani mai suna Adam Babukarna, ya bayyanawa muryar Amurka cewar ‘yan kunar bakin waken da suka kai harin sun mamaye Sojojin ne kuma yace tunda Sojojin Najeriya da na Nijar suka fice daga garin Damasak, ‘yan Boko Haram, ke kai hare hare jefi jefi.

Ya kara da cewa abunda ya kawo tsaiko shine kogin Komadougou wanda yake iyakar tsakanin Najeriya, da Nijar ta jahar Yobe ta inda ‘yan kungiyar ta Boko Haram ke yin amfani da Kwale Kwale suna ketarawa.

Tashin Boma Bomai bai hana makarantu da kasuwani sun bude ba kuma bada Sojoji da ‘yan kunar bakin waken babu wanda ya rasa ransa.

An Samu Tashin Boma Bomai a Jamhuriyar Nijar- 3'01"

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG