Jami'yyun adawa a Jamhuriyar Nijar sun bukaci a tsige frai ministan kasar daga mukaminsa saboda zargin gwamnatinsa da gazawa wajen kaddama da ayyuka da dama da suka shafi tafiyar da kasar, da kuma kasawa wajen tsaren zabubbukan 2021.
Kimanin ‘yan majalisa 35 na bangaren adawa ne suka saka hannu akan takardar da suka shigar a gaban majalisar dokokin kasar, domin bukatar tsige Brigi rafini.
'Yan adawa sun kuma zargi gwamnatinsa da gazawa wajen shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi kasar.
Masu rinjaye wadanda ke kallon wannan yunkuri a matsayin wata alamar da ke fayyace mizanin dimokradiya a Jamhuriyar Nijar cewa suke ga ‘yan hamayya da a zuba a gani.
Daga cikin kujeru 171 na wakilici a majalisar dokokin kasa ‘yan adawa na da kujeru 35 yayin da PNDS Tarayya da kawayenta ke da kujeru 136.
A ka’idance, nan da sa'o'i 48 ne ya kamata bangarori su tafka mahawara kafin daga bisani a yi kuria’r raba gardama kan wannan batu.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Your browser doesn’t support HTML5