Yakin Neman Zama Dan Takarar Shugaban Kasa A Amurka

DEM 2016 Clinton

Yan takarar shugaban kasa a Amuraka sun dukufa kai da kafa wajen yakin neman zaben da za’a yi gobe Talata idan Allah ya kaimu, zaben da ake cewa Super Tuesday domin jihohi goma sha daya ne zasu yi zaben.

Wadannan jihohin sune ke wakiltar rubi guda na wakilan da dan takara ke bukata wajen baban taron jam’iyun Democrat da Republican da za’a yi a watan Yuli idan Allah ya kaimu domin samun jam’iyun su tsayar dasu ‘yan takara a zaben shugaban kasar da za’a yi a watan Nuwamba idan Allah ya kaimu.

In baicin jihar Texas masu lura da harkokin siyasar Amirka sunyi hasashen cewa rikakken attajirin nan Donald Trump shine ke kan gaba wajen farin jinni

Ta bangaren jam’iyar Democrat kuma, tsohuwar sakataren harkokin wajen Amirka Hillary Clinton, ita aka yi hasashen zata zama zakara a jihohi goma sha daya. Yanzu haka dai Hillary Clinton tana murnar gagarumin nasarar data samu a jihar South Carolina.