Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Wasu 'Yan Fashi, 'Yan Nijar A Lagos


‘Yan sandan suntiri a unguwar Tinubu dake Lagos Island, jihar Ikko sun kame wasu matasa ‘yan Nijar su 5, bisa laifin fashi.

Dukansu matasan sana'ar gadi su ke yi a kasuwar Balogun kafin haduwarsu da wani mai suna Isa, dan jihar Borno wanda ake zargi shi ne ya dulmayad da su cikin wannan harkar. Kuma dukan su shekarunsu sun kama daga 21 zuwa 23.

A halin da ake ciki, ‘yan fashin da ake zargi sun fadawa jami’an ‘yan sanda cewa su dama sun je Najeriya ne da niyyar su yi arziki, a cewar kamfanin dillancin labaran New Telegraph.

Daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Musa, wanda ya kwashe shekara 15 a Lagos ya fadi cewa da sana’ar kabu-kabu ya ke yi amma shekaru 5 da su ka wuce ’yan sanda suka kwace masa abun hawan, daga nan ya koma sana’ar tuka mota.

Musa ya kuma ce da ma can sauran na fashi tun kafin ya san su. Watanni biyu da suka wuce ya hadu da su. Ya kara da cewa sun raba kason naira 140,000 daga fashin da su ka yi a wurare biyu. “Manyan kantunan kaya nan suka fi maida hankali” a cewa Musa.

Shi kuma shugaban, yan fashin mai suna Alisuma, cewa yayi ya je Najeriya ne da niyyar yin aiki amma aikin gadi bai iya biyan bukatunsa ba, don haka shi da abokansa suka yanke shawarar fara yin fashi don su sami abin da za su tura gida.

Alisuma ya kara da cewa, iyayen su na ganin akwai kudi a Najeriya, shi ya sa suke sa ran wani abu mai tsoka daga duk wanda ya je aiki Najeriya.

XS
SM
MD
LG