Idan ana maganar babban gini, to ana maganar babban aiki, wadannan sune ginanuwa da sukafi tsada a duniya, wajen kashe kudi don gina su. Wani dakin taro na Vancouver Convention Center, an kamala gina wannan ginin mai hawa 6 a shekarar 2009, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka milliyan $883M.
Ofishin jakadanci Amurka dake kasar Ingila, ana sa ran a kammala ginin a karshen wannan shekarar andai fara aikin ne a shekarar 2008, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka milliyan $902M. Sai ginin Chifley Tower, na kasar Sydney, mai hawa 42, an gina shi a shekarar 1992, wanda yaci kudi Billiyan $1.2 a waccan shekar an kiyasta kudin da za’a iya gina irin shi a yanzu da zai kai dallar Amurka milliyan $903M.
Shi kuwa ginin MGM Grand Macau, na kasar China, wanda ke da dakuna 600 da hawa 28, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka milliyan $975M. Haka ginin shelkwatar Banki Amurka, dake birnin New York, wanda shine ginin da yafi kowanne tsawo a birnin, yana da tsawon mita 1,200, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1B. Sai Otel din Niagara Falls Hilton Towers, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1B shima.
Ginin Antilia, a babban birnin India, na wani hamshakin mai kudin kasar Mukesh Ambani, ginin nada hawa 27, an kiyasta kudin ginin da ya kai dallar Amurka billiyan $1B. Ginin Elbphilharmonie, an kiyasata kudin da zai ci da suka kai billiyan $1.02B amma abun ban mamaki shine gini zai ci karin kudi da suka kai dallar Amurka milliyan $678M.